Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Nemi Majalisar Dokoki Ta Dakatar Da Harajin Da Ake Karba A Hannun Masu Shan Mai


Shugaban Amurka, Joe Biden.
Shugaban Amurka, Joe Biden.

Farashin man fetur ya haifar da kaso mafi girma na hauhawar farashin kayayyakin masarufi, hayar gidaje, farashin tikitin hawa jiragen sama da sauran abubuwa da dama.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga Majalisar dokokin kasar da ta amince da dakatar da harajin man fetur na kasar na tsawon watanni uku - daga Yuli zuwa Satumba - don taimakawa Amurkawa su shawo kan matsalar tsadar rayuwa.

Harajin shi ne senti 18.4 akan galan (lita 3.8) na man fetur, wanda ya kara dala $2.76 ga farashin cika galan 15 na yau da kullun ga masu ababen hawa a famfunan tashar shan mai.

Rage harajin zai zama senti 24 kan galan na man dizal.

Farashin man fetur ya haifar da kaso mafi girma na hauhawar farashin kayayyakin masarufi, hayar gidaje, farashin tikitin hawa jiragen sama da sauran abubuwa da dama.

Biden ya kuma yi kira ga jihohi 50 na kasar da su ma su dakile harajin iskar gas na wani lokaci.

Tuni dai wasu jihohin suka yanke harajinsu, yayin da wasu ke bayyana fargabar cewa ragewar za ta shafi kudaden shigar da ake bukata na gina manyan tituna da gyare-gyare.

Rage harajin tarayya na kudin man fetur zai sa a rasa kudin kula da manyan hanyoyin kasar dala biliyan 10.

Sai dai masu adawa da wannan kira na Biden musamman ‘yan Republican da wasu daga cikin ‘yan Democrat, sun ce matakin ba zai yi wani tasiri ba.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar Dattawan Amurka Mithc McConnell, ya kwanta tsare-tsare gwamnatin ta Biden a matsayin marasa kan gado.

XS
SM
MD
LG