A jiya Laraba Hukumar Lafiya ta Duniya – WHO, ta ayyana cutar Coronavirus a matsayin annoba, biyo bayan bullar cutar a kasashe 114.
Yayin da shugaban Amurka ke fuskantar matsin lamba kan bukatar daukar matakai da zasu hana yaduwar cutar Coronavirus, shugaban ya gabatar da wani jawabi wanda aka yada ta gidajen talabijan.
Gwamnatin kasar Italiya ta fadada dokar takaita tafiye-tafiye a duk fadin kasar, inda ta killace mutum miliyan 60 a kokarin shawo kan yaduwar cutar Coronavirus.
Jiya Litinin kasuwannin hannayen jari sun fadi warwas a fadin duniya, saboda wasu manyan dalilai guda biyu.
Kasar Saudiyya ta dauki matakin rufe makarantu a yau Litinin a matsayin rigakafin yaduwar cutar Coronavirus.
Jiya lahadi, Shugaba Buhari na Najeriya ya aika wa shugabbanin kasashen Iran da Korea ta Kudu, da frai ministan Italiya sakonnin jaje, inda ya nuna matukar juyayi kan karuwar yaduwar cutar Coronavirus a kasashensu.
Dakarun Amurka na taimaka wa wajen neman rigakafin cutar Coronavirus da ke saurin kisa, yayin da likitoci ke da sauran watanni 12 zuwa 18 a yunkurin da suke yi na ganin sun samar da rigakafin cutar ga jama’a.
Kasar Saudiyya ta sake bude masallatai biyu mafiya tsarki a addinin Musulunci, wato Al-Haram da ke Makkah da kuma Al-Masjid al Nabawy da ke birnin Madina.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.