Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Kasuwannin Hannayen Jari a Duniya Sun Fadi


Wasu masu shaguna a China, wadanda ke fama da rashin siyan kayayakinsu sakamakon bullar tutar Coronavirus.
Wasu masu shaguna a China, wadanda ke fama da rashin siyan kayayakinsu sakamakon bullar tutar Coronavirus.

Jiya Litinin kasuwannin hannayen jari sun fadi warwas a fadin duniya, saboda wasu manyan dalilai guda biyu.

Na farko dai shi ne farashin man fetur da kuma galabaitar da tattalin arziki yayi saboda cutar Coronavirus wadda ke ci gaba da yaduwa a kasashe sama da 100.

Muhimman hada-hadar da aka yi a kasuwar hannun jari a birnin New York jiya dai sun fadi da sama da kashi 7 cikin 100, biyo bayan faduwar kashi biyar cikin 100 a wasu kasuwannin hannun jari na nahiyar Asiya.

Yayin da kasuwannin hannun jarin nahiyar Turai suka tashi da kusan faduwar kashi 8 cikin 100.

Ita kuma Kasuwar hannun jari da aka fi sa wa ido, wato Dow Jones da ke dai-dai da hannayen jarin wasu manyan kamfanonin Amurka 30, ta tashi da maki 2,000 kawai, wanda ke dai-dai da faduwar kashi 7.9 cikin 100.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG