Rahotanni daga jihar Kano na cewa ‘yan daba sun hana a gudanar zabe a wasu mazabun jihar.
Kammala zaben gwamna da ake yi a jahar Filato na gudana cikin tsauraran matakan tsaro.
A jihar Bauchi sake zabukan da ba a akammala su ba a yankunan kananan hukumomin jihar ya gudana cikin yanayi mai kyau musamman ma idan akayi la’akari da samun yawan fitowar mutane masu son kada kuri’a.
Hedkwatar sojojin Najeriya ta kafa wani kwamitin bincike karkashin jagorancin wani babban Hafsa Manjo Janar T.A. Gagariga, don binciko zarge zargen da ake yi wa sojin lokacin zaben 2019.
Bayan da wata babbar kotu a jihar Adamawa ta ba da umarnin dakatar da zaben jihar da za a kammala, hukumar zaben ta INEC reshen jihar ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar wannan hukunci.
An bude wani sabon babi a takaddamar sakamakon zaben Shugaban Kasa a Najeriya, bayan da jam'iyyar PDP ta shigar da kara a kotun daukaka kara don kalubalantar ayyana Shugaba Buhari na jam'iyyar APC da aka yi a matsayin wanda ya ci zaben.
Jayayya kan makomar zaben gwamnan jahar Bauci sai abin da ya yi gaba, duk kuwa da shirin bayyana sakamakon zaben a yau dinnan, bayan da hukumar zabe ta INEC ta sauya shawara ta wajen tsame jahar Bauci daga jerin jahohin da ta ayyana zabukansu marasa kammala.
Jami’iyyar PDP a jahar Nasarawa ta ce za ta je kotu saboda rashin gaskiya da ta ce anyi mata a zaben gwamna da aka gudanar makon jiya.
Domin Kari