Saneta Useni wanda ya rike mukamai da dama karkashin mulkin soja da ya hada da ministan babban birnin tarayya Abuja, yace dokar da majalisa ta kafa da shugaban kasa ya sawa hannu domin ba matasa damar tsayawa takara da ake kira “Not Too Young To Run” an kafa ta ne da nufin ba matasa lokaci su kara nazarin harkokin mulki kafin shiga siyasa gadan gadan, sabili da haka aka bada tsawon shekaru kafin ta fara aiki.
Janar Useni wanda ya kasance dan takakarar gwamna mafi yawan shekaru a zaben na bana, yace, yana jin yafi wadansu masu jini a jika kuzari, sabili da haka baya ganin shekarunsa a matsayin wata kalubala. Dangane kuma da delilin da yasa bai nemi tsayawa takarar shugaban kasa, ba ganin shekarunsa da kuma mukamai da ya rike a baya, Janar din da aka fi sani da J.T. Useni yace, lokacin da al’ummarsa suka neme shi ya tsaya takara, sun bukace shi ne ya tsaya takarar gwamna, abinde kuma ya yi ke nan.
Daga cikin matsalolin da yace zai maida hankali a kai idan aka zabe shi gwamna akwai batun shawo kan matsalar harkokin tsaro da samar da ayyukan yi tsakanin matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.
Yace jihar Plato ta yi fama da tashe tashen hankali da rikicin addini da kabianci da suka gurguntar da harkokin noma, da kasuwanci da tattalin arzikin jihar, sabili da haka akwai bukatar samun wanda yake da karfin hali da kwarewa da kuma hangen nesa, kuma bisa ga cewar shi, ya mallaki wadannan duka.
Saurari cikakkar hirar su da Alheri Grace Abdu
Facebook Forum