Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Ta Amince Da Dokar Kama Bakin Haure Da Ake Zargi da Aikata Laifuka


Congress Immigration
Congress Immigration

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu akan kudirin dokar da Majalisar ta amince da shi, wanda ya samu goyon bayan bangarorin biyu.

Majalisar ta Amurka ta amince da kudirin doka da Trump ya sanya wa hannu da ke bukatar a tsare ko kama bakin haure musamman bakin hauren da ake zargi da aikata laifukan sata da kuma sauran laifuka .

Kudirin dokar da aka yi wa lakabi da “Passage of the Laken Riley Act”, da aka sanya wa suna bayan da wani dan kasar Venezuela ya kashe wata dalibar jinya a jihar Georgia, a bara.

Manufofin shige da fice sau da yawa na zama daya daga cikin batutuwan da ke da tushe a majalisa, amma wani muhimmin bangare na 'yan jam’iyyar Democrat marasa rinjaye a majalisar sun kada kuri’ar amincewa da kudirin dokar tare 'yan Republican da kuri'u 263-156.

A halin da ake ciki kuma, Trump ya kaddamar da wasu tsauraran umarni da nufin rufe kan iyakar Amurka da Mexico inda miliyoyin bakin haure ke shiga Amurkar, Trump ya kuma soke shirin tsugunar da 'yan gudun hijira, kuma gwamnatinsa ta yi nuni da cewa tana da niyyar gurfanar da jami'an tsaron cikin gida wadanda ba sa aiwatar da sabbin manufofin Trump na shige da fice.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG