Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Daukaka Kara Kan Hukuncin Zama Dan Kasa Ta Hanyar Haihuwa


Wani alkalin tarayya ya dakatar da yunkurin Trump na takaita damar zaman dan kasa ta hanyar haihuwa na wucin gadi.

A jiya Alhamis, Shugaban Amurka Donald Trump yace gwamnatinsa za ta daukaka kara a kan hukuncin da wani alkalin kotun tarayya ya yanke wanda ya dakatar da yunkurin takure damar zama dan kasa ta hanyar haihuwa.

“Tabbas zamu daukaka kara a kan hukuncin,” kamar yadda Trump ya shaidawa manema labarai a ofishinsa (Oval Office) lokacin da aka tambaye shi game da hukuncin da alkalin lardin jihar Washington John Coughenour ya yanke, wanda yace karara umarnin shugaban ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar.”

A jiya Alhamis wani alkalin tarayya ya dakatar da yunkurin Trump na takaita damar zaman dan kasa ta hanyar haihuwa na wucin gadi.

Hukuncin zai dakatar da tursasa amfani da umarnin zartarwar dake cike da cece-kuce da Trump ya rattabawa hannu sa’o’i bayan rantsar da shi a kan mulki a wa’adi na 2, tsawon kwanaki 14.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG