Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohuwar ‘Yar Democrat Tulsi Gabbard Ta Nuna Goyon Baya Ga Donald Trump

Tsohon shugaba Trump, hagu da Gabbard, dama (Photo by JEFF KOWALSKY
Tsohon shugaba Trump, hagu da Gabbard, dama (Photo by JEFF KOWALSKY

Gabbard ita ce ‘yar majalisar daya tilo da ta ki kada kuri’a a lokacin da majalisar wakilai ta tsige Trump saboda wasu huldodi da ya yi da Ukraine.

Tsohuwar ‘yar majalisar wakilai karkashin jam’iyyar Democrat Tulsi Gabbard ta bayyana goyon bayanta ga tsohon Shugaban Amurka Donald Trump.

Wannan mataki da Gabbard ta dauka ya kara nuna yadda ‘yar siyasar wacce ta nemi tikitin jam’iyyar a zaben 2020 take kara nesanta kanta da jam’iyyar ta Democrat.

A ranar Litinin Gabbard ta bayyana tare da Trump a birnin Detroit na jihar Michigan inda ta ce, “Trump ya san nauyin da ya rataya a wuyansa na daukar dawainiyar rayuwar kowane Ba’amurke.”

Gabbard ta wakilci jihar Hawaii a majalisar wakilan har tsawon shekaru hudu karkashin jam’iyyar Democrat ta kuma nemi tikitin tsaya wa takarar shugaban kasa a shekarar 2020.

A shekarar 2022 ta fice daga jam’iyyar ta kuma taya manyan ‘yan takarar Republican yakin neman zabe a sassan kasar.

Gabbard ita ce ‘yar majalisar daya tilo da ta ki kada kuri’a a lokacin da majalisar wakilai ta tsige Trump saboda wasu huldodi da ya yi da Ukraine.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG