Trump mai shekaru 78 ya zabi Vance mai shekaru 39 a matsayin abokin tafiyarsa a takarar shugaban kasa a watan Nuwamban 2024.
Daga cikin mutane uku da ake sa ran Trump zai zaba a matsayin mataimaki, akwai Sanata J.D. Vance na jihar Ohio, Sanata Marco Rubio na jihar Florida da gwamnan North Dakota Doug Burgum.
Hukuncin na zuwa ne kwana biyu bayan da Trump ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wani dan bindiga ya yi yunkurin halaka shi.
Wani abokin karatun Thomas Matthew Crooks, matumin da ake zargi da yunkurin kashe Trump, ya bayyana shi a matsayin wanda aka tsangwama, ba mai hulda da shi sosai, yayin da masu bincike suka gano ababen fashewa a cikin motar Crooks da gidansa.
Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yakin neman zaben tsohon Shugaban kasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.
Ofishin yakin neman zaben tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa, tsohon Shugaban kasar ya samu rauni a ka yau Asabar, amma yana “lafiya” bayan da aka harba bindiga a wajen da ya ke wani gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania.
Alamu na nuna an harbi dan takarar jam'iyyar Republican kuma tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani taron yakin neman zabe a garin Butler da ke jihar Pennsylvania a Amurka ranar Asabar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya marabci shugabannin kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO a birnin Washington a ranar Talata don gudanar da wani taron shekara shekara wanda zai bai wa jam'iyyar Demokrat da ke fama da rikici damar shawo kan kawayenta na cikin gida da waje cewa zai iya jagoranci.
A jiya Alhamis Amurka tayi bikin ranar samun 'yancin kai na tsawon kusan karni biyu da rabi, hutun ranar 4 ga watan Yuli da ta kasance ranar da ta ayyana cin gashin kanta daga Birtaniya.
An kama tsohon mai taimaka wa Donald Trump kan harkokin siyasa, Steve Bannon a jiya Litinin bayan da ya kai kansa ga hukumomi a gidan yarin tarayya saboda kin amsa sammacin da Majalisar Wakilai ta yi masa lokacin da take gudanar da bincike kan tashin hankalin da aka yi a ranar 6 ga Janairu, 2021.
Kotun kolin ta yanke hukunci jiya Litinin cewa, shugabannin Amurka suna da kariya daga tuhuma kan laifukan da suka aikata lokacin da suke kan karagar mulki, kuma suna da cikakkiyar kariya daga gurfanar da su a gaban kotu a kan abinda su ka aikata yayinda su ke gudanar da aikin Shugaban kasa.
Hukumar Kwallon kafa ta Amurka ta yi Allah wadai da kalaman nuna wariyar launin fata ga ‘yan wasanta a ranar Alhamis, bayan da Panama ta yi nasara a kan Amurka da ci 2-1 a gasar cikin kofin Copa America.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.