Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tayi Bikin Ranar Samun 'Yancin Kai


Bikin 'Yancin Kan Amurka
Bikin 'Yancin Kan Amurka

A jiya Alhamis Amurka tayi bikin ranar samun 'yancin kai na tsawon kusan karni biyu da rabi, hutun ranar 4 ga watan Yuli da ta kasance ranar da ta ayyana cin gashin kanta daga Birtaniya.

Bikin na ranar hudu ga watan Yuli, biki ne kuma na tabbatar da zama dan kasar Amurka. Amurkawa a ko’ina su ke a duniya suna daukar wannan rana da muhimmancin gaske da gudanar da shagulgula iri dabam dabam da ke nunawa da kuma jaddada so, da kishin kasa.

Wasan Wuta Mai Dauke Da Launuka Daban Daban Yayin Bikin Murnar Zagayowar Ranar Yankin Kan Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00

An gudanar da bikin a sassan Amurka da baje wasan wuta da ya rika tartsatsi da haske a birane da garuruwa, manya da kanana. An kuma yi faretin murnar democradiyyar kasar a ko ina a fadin Amurka, da jadada 'yancin fadin albarkacin baki, 'yanci kada kuri’a, ko akasin haka, da kuma 'yancin yin addini ko akasin haka.

Bukin 'Yancin kan Amurka
Bukin 'Yancin kan Amurka

Tun da farar safiyar Alhamis da ga ko ina suka hallara a farfajiyar ginin Majalisa Capitol Hill domin gane wa idanun su irin kayataccen bukin da aka gudanar a wurin, da ya hada da fareti, harba bindiga, kade kade da raye raye da wake waken shahararrun mawakan kasar, da wasan wuta mai dauke da launuka iri dabam dabam da ya rika haske sararin samaniya.

Harbe-Harben Bindiga Yayin Gudanar Da Bikin Ranar Samun 'Yancin Kan Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Kimanin mutane dubu goma sha daya su ka zama 'yan kasar Amurka a hukumance a makon da ake hutun gudanar da shagulgulan, adadin da ya ninka akan na shekara guda ta da wuce. Hukumar dan kasa ta Amurka da ta shigi da fici, ta shirya bukukuwan zama dan kasa har dari da casa’in da biyar a sassan duniya, tsakanin 28 ga watan Yuni da 5 ga watan Yuli.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG