Daruruwan mutane ne suka gudanar da faretin bikin ranar Isra'ila a birnin New York a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi kira da a sako mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.
Falasdinawa a birnin Rafah da ke kan iyaka sun ba da rahoton kazamin fada a 'yan kwanakin nan, yayin da sojojin Isra'ila ke kara fadada hare-haren da suke kai wa a kudancin kasar, tare da kwace iko da daukacin iyakar Gaza da Masar.
Shugaban Amurka Joe Biden a sakaye ya baiwa Kyiv damar harba makaman da Amurka ta kai musu cikin kasar Rasha, tare da sharadin cewa a kusa da kan iyaka da yankin da ke kusa da birnin Kharkiv na arewacin Ukraine kawai za a kai harin, in ji jami'an Amurka a ranar Alhamis.
Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka samu da laifi a ranar Alhamis a lokacin da wani alkali a birnin New York ya same shi da laifin saka bayanan karya a takardun hada-hadar kudadensa don ya boye batun kudin toshiyar baki da ya biya wata jarumar fina-finan batsa gabanin zaben 2016.
A ranar Alhamis ne za a kashe wani mutum mai shekaru 50 da haihuwa ta hanyar yin allura mai guba a jihar Alabama da ke Kudancin Amurka bisa laifin kashe wasu tsofaffin ma'aurata.
"Abin da ke faruwa a Gaza ba kisan kare dangi ba ne, mun yi watsi da hakan," in ji Biden a wani taron watan al'adun Yahudawa na Amurka a fadar White House.
A cikin kwanaki masu zuwa, ana sa ran sojojin Amurka da ke gabashin tekun Bahar Rum za su hada karshen daya gefen harabar wata dirkekiyar tashar jirgin ruwa - mai tsawon filayen wasan kwallon kafa na Amurka guda biyar a gabar teku a arewacin Gaza.
Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell ya fada a ranar Litinin cewa gwamnatin Biden ba ta ganin akwai yuwuwar Isra’ila ta samu “cikakkiyar nasara” wajen fatattakar Hamas a yankin Gaza na Falasdinu.
Shugaba Joe Biden ya fada jiya Laraba cewa ba zai aika da muggan makamai ga Isra'ila da za ta iya amfani da su wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan Rafah ba, wanda yake tungar karshe ta Hamas a Gaza, saboda nuna damuwa kan yadda zai afka kan fararen hula fiye da miliyan 1 da ke fakewa a wurin.
A ci gaba da shari'ar tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, wadda ake yi a New York, tauraruwar fina finan batsa, Stormy Daniels, ta yi bayani mai cike da batsa jiya a kotun.
Duk da cijewar da tattaunawar Isira'ila da Hamas ta yi, Amurka na fatan bangarorin biyu za su cimma jituwa kan sauran bambancin da ke tsakaninsu don a samu tsagaita wuta.
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dallas na kasar Amurka, domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024 wanda kungiyar kamfanoni kan Afirka ta shirya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.