Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Goyon Bayan Isra'ila Sun Yi Tattaki A Birnin New York


Dubban magoya bayan Isra’ila sun yi tattaki a titin Manhattan ta Fifth Avenue a jihar New York.
Dubban magoya bayan Isra’ila sun yi tattaki a titin Manhattan ta Fifth Avenue a jihar New York.

Daruruwan mutane ne suka gudanar da faretin bikin ranar Isra'ila a birnin New York a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi kira da a sako mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

Dubban magoya bayan Isra’ila sun yi tattaki a titin Manhattan ta Fifth Avenue, wani titin ‘yan kasuwa, domin gudanar da fareti na shekara-shekara, suna rike da tutar Isra’ila mai launin shudi da fari, suna rera taken “dawo da su gida”.

Masu shirya taron sun ce suna son su nuna goyon bayansu ga al'ummar Isra'ila game da mutane sama da 120 da Hamas ta yi garkuwa da su tun ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka aika da sakon gaggawa ga duniya: 'Ku dawo da su gida yanzu!''.

Harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba ya yi sanadin mutuwar mutane 1,189, galibi fararen hula, kuma sun yi garkuwa da mutane 252, kamar yadda alkaluman hukumomin Isra'ila ta nuna a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Harin ramuwar gayya na Isra'ila ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 36,439 a Gaza, galibinsu mata da kananan yara, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin Hamas.

Malam Eron Galzor mai shekaru 51 ya shaidawa AFP cewa "A yanzu haka Isra'ila na fuskantar hari."

"Sakonmu a bayyane yake -- a hallaka Hamas, a dawo da wadanda aka yi garkuwa da su gida." In ji magajin garin, Eric Adams, a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG