Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kashe Wasu Mutum Biyu Da Aka Samu Da Laifin Kisan Kai A Jihar Alabama


Gadon allura mai kisa
Gadon allura mai kisa

A ranar Alhamis ne za a kashe wani mutum mai shekaru 50 da haihuwa ta hanyar yin allura mai guba a jihar Alabama da ke Kudancin Amurka bisa laifin kashe wasu tsofaffin ma'aurata.

An yanke wa Jamie Ray Mills hukuncin kisa ne a shekara ta 2007 saboda laifin kashe Floyd Hill mai shekaru 87 da kuma matarsa Vera Hill, mai shekaru 72 a lokacin wani fashi.

Mills ya aikata kisan ne da adduna da karafe.

An yanke wa matarsa Joann Mills hukuncin daurin rai da rai a gidan yari ba tare da neman afuwa ba saboda hannu a kisan gillar da aka yi a shekara ta 2004.

An shirya kashe Mills a yammacin Alhamis a cibiyar gyara hali na Hulman Da Ke Atmore, a cewar sashen gyaran Alabama.

Zai kasance fursuna na biyu da aka yankewa hukuncin kisa a Alabama a wannan shekara.

A watan Janairu, Alabama ta aiwatar da hukuncin kisa na farko a Amurka ta hanyar amfani da iskar gas, sai dai za a kashe Mills ne a hanyar yin allurar guba.

A cewar wani bincike na baya-bayan nan, kashi 53 na Amurkawa suna goyon bayan hukuncin kisa ga wanda aka samu da laifin kisan kai, wanda shi ne matakin mafi karanci tun 1972.

An soke hukuncin kisa a jihohi 23, yayin da gwamnonin jihohi shida wato Arizona, California, Ohio, Oregon, Pennsylvania Da Tennessee suka dakatar da amfani da shi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG