Har yanzu babu tabbacin ko za a yanke hukumci kan shari'un da ke gaban kotu inda ake tuhumar zababben Shugaban kasar Amurka da aikata wadansu laifuka.
Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya zabi Scott Turner, tsohon dan wasan kwallo wanda ya taba rike mukami a fadar white House a lokacin shugabancin Trump na farko, da ya jagoranci bangaren gidaje da raya birane.
Majalisar birnin Los Angeles baki daya ta zartar da dokar “baiwa bakin haure kariya” don kare bakin haure da ke zaune a birnin, manufar da za ta haramta amfani da albarkatun birnin da ma'aikatasa don aiwatar da dokar shige da fice ta tarayya.
Ana sa ran kwamitin ladabtarwa na Majalisar Wakilan Amurka zai gana gobe Laraba domin yanke shawara kan ko ya fitar da rahoton bincikensa kan tsohon dan majalisa Matt Gaetz ko a’a.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi watsi da wasu sabbin zarge-zarge da Rasha ta yi cewa, Amurka na sa yakin da ake yi a Ukraine maida yankin wani wuri mai hatsarin gaske.
Gwamnatin Biden ta sahalewa Ukraine yin amfani da makaman da aka kera a Amurka wajen kai hare-hare cikin Rasha, kamar yadda wasu jami’an Amurka 2 da wata majiya dake da masaniya game da shawarar suka bayyana a jiya Lahadi
A yayin da zababben shugaban Amurka ke shirye shiryen kama aiki, wani ingantaccen tsari na tafe na ganin an mika mulki daga gwamnati mai barin gado zuwa ga sabuwar gwamnati mai kamawa cikin kwanciyar hankali.
Zababben shugaban Amurka Donald Trump na aza kaimi wajen saurin hada hancin gwamnatin shi, da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar Republican, wadanda da mafi yawansu suka kasance masu biyayya gare shi a shekaru hudun da ya kasance baya ofis.
Ana sa ran zabebban shugaban Amurka Donald Trump ya dauki dimbin matakan zartarwa a ranarsa ta farko a fadar white house domin tsaurara dokokin shige da fice tare da rushe babban shirin Joe Biden na shiga kasar ta hanyar doka, kamar yadda wasu majiyoyi 3 da suka fahimci batun suka shaidawa Reuters
Da yammacin jiya Lahadi, zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai dawo da jami’in kula da shige da ficen nan mai ra’ayin rikau Tom Honan ya zama mai kula da kan iyakokin kasar a gwamnati mai shigowa.
A ranar Asabar ministan tsaron Lithuana yace, kada kasashen tarayyar turai su sake yin kuskuren haifar da shinge tsakanin su da zababben shugaban Amurka Donald Trump, maimakon haka kamata yayi su hada kai kan al’amurran da zasu amfane su baki daya.
Hukumomin tarayya da na jiha na binciken wani sakon wasika na nuna wariyar launin fata da aka rika turawa a boye ga Amurkawa bakar fata a sassan kasar.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.