A yayin ziyarar, sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta kara inganta hadin gwiwar Amurka da Afirka tun bayan taron Shugabannin Amurka da Afirka, da suka hada da yanayi, abinci, da kiwon lafiya.
An kebe kowace ranar Litinin na uku (3) a watan Jana'iru a matsayin ranar hutu don tunawa da Dakta Martin Luther King Junior wanda ya jagoranci jerin zanga-zangar lumana tsakanin shekararun 1950 zuwa shekarun 1960.
Sojojin Amurka da na Birtaniyya sun yi ruwan bama-bamai kan 'yan Houthis da ke samun goyon bayan Iran a Yemen a ranar Alhamis, a wani gagarumin harin ramuwar gayya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen yaki na Tomahawk da jirgin ruwan yaki da na karkashin ruwa, in ji jami'an Amurka.
Mahaifiyar Melanie Trump, matar tsohon Shugaban kasar Amurka Donald. Trump, Amalija Knavs, ta rasu, kamar yadda Trump ya tabbatar a wata sanarwa da aka wallafa a X, wanda a da ake kira Twitter. Amalija ta rasu tana da shekaru 78.
A jiya Lahadi manyan shugabannin Majalisar Dokokin Amurka suka amince da kasafin kudin da gwamnatin tarayya zata kashe a shekarar 2024 na dala triliyan 1 da digo 6.
Wani matashi dan shekara 17 ya bude wuta a wata karamar makarantar sakandare ta Iowa a Amurka, a rana ta farkon komawa makaranta bayan hutun hunturu, inda ya kashe wata yarinya ‘yar aji shida tare da raunata wasu biyar a ranar Alhamis yayin da daliban suka yi shinge a ofisoshi a firgice.
A jiya Talata tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya daukaka kara kan hukuncin da sakatariyar harkokin wajen jihar Maine ta jam’iyyar Democrat ta yanke, na haramta masa takara.
"An tabbatar da cewa an kashe Maalim Ayman ne a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya tare da taimakon sojojin Amurka suka yi a ranar 17 ga watan Disamba," in ji Daud Aweis a shafinsa na X da yammacin ranar Alhamis.
A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Hada-Hadar Kudi ta Amurka (SEC) ta gurfanar da dan kasuwan nan na Najeriya Dozy Mmobuosi da wasu kamfanoni uku wanda shi ne shugabansu, inda ake zargin su da damfarar masu zuba jari.
"Kotun koli ta Colorado ta fitar da wani hukunci mai cike da kura-kurai a daren yau kuma za mu shigar da kara cikin gaggawa zuwa kotun kolin Amurka." in ji mai magana da yawun yakin neman zaben Trump
Isira’ila ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a ranar Talata tare da ci gaba da kai hari ta kasa akan mayakan Hamas a Zirin Gaza, yayin da Amurka ta hada kawayenta don kare hanyoyin jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya daga ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran a Yemen.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.