'Yan majalisar dokokin Amurka sun kada kuri'ar tsige kakakin Majalisar Wakilai daga mukaminsa, wannan shi ne karon farko da aka taba ganin haka a tarihin Amurka.
A yayin da aka fara taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin D!uniya wanda ke samun wakilcin shugabannin duniya, masu harkokin kasa da kasa sun bukaci sauyi daga kasashe masu karfi zuwa kananan kasashe irin na Afirka.
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya hado kan shugabannin kasashen duniya a birnin New York a wannan mako, inda tarukan da za a gudanar a ranar bude taron, za su mai da hankali kan kara kaimi wajen cimma muradun samar da ci gaba a duniya.
Biden ya yi ƙira da a sanya Najeriyar cikin mambobin ƙungiyar kasashen ta G20.
'Yan Republican a majalisar wakilai sun zargi Biden da cin moriyar hada-hadar kasuwancin iyalinsa a kasashen waje.
A yau ranar Litinin 11 ga watan Satumba ne Amurka ta cika shekaru 22 da aka kai mata hare-haren ta'addanci wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 3,000.
Dutsen Kilauea da ke tsibirin Big Island na Hawaii ya sake barkewa da aman wuta ne a yammacin Lahadin da ta gabata, inda a halin yanzu aman wutar da ya ke yi a kewayen dutsen ne kawai, kamar yadda hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka (USGS) ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata.
Akalla mutum 16 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a ranar Laraba, bayan da Rasha ta yi luguden wuta kan wata kasuwa a wani birni a gabashin Ukraine, in ji jami'ai.
Uwargidan shugaban Amurka Jill Biden ta kamu da cutar COVID-19 kuma a halin yanzu tana fama da alamu masu sassauci, in ji Fadar White House a ranar Litinin.
Mataimakiyan sakatarin harkokin wajen Amurka mai kula da sha'anin Afrika Molly Phee ta bayyana cewa Ghana da Amurka za su ci gaba da hada hannu wajen tabbatar da mayar da dimokradiyya a Nijar.
'Yan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Republican sun fara muhawara a daren Laraba a babban taron farko na zaben Shugaban kasa na shekara mai zuwa.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.