Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

 Za A Kaddamar Da Binciken Duba Yuwuwar Tsige Shugaba Biden - McCarthy


Shugaban majalisar Wakilai McCarthy
Shugaban majalisar Wakilai McCarthy

'Yan Republican a majalisar wakilai sun zargi Biden da cin moriyar hada-hadar kasuwancin iyalinsa a kasashen waje.

Kakakin Majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy ya sanar a ranar Talata cewa ‘yan majalisar wakilai za su fara binciken duba yuwuwar tsige Shugaba Joe Biden, don fadada bincike kan zargin da ake yi wa shugaban na cin moriyar harkokin kasuwancin dansa Hunter a kasashen ketare.

"Wadannan zarge-zargen sun nuna dabi’ar rashawa," abinda McCarthy ya fada wa manema labarai kenan.

"Mun gano cewa Shugaba Biden ya yi wa jama'ar Amurka karya game da abinda ya sani kan mu'amalar kasuwancin iyalinsa na kasashen waje. Wadanda suka shaida lamarin sun fadi cewa an yi waya da shi lokuta da yawa, ya kuma je liyafar cin abinci, lamarin da ya sa dansa da abokan kasuwancinsa samun motoci, da miliyoyin daloli,” in ji McCarthy a yayin wani taron manema labarai.

Sai dai har yanzu kwamitocin Majalisar da yawa ba su sami wata hujja akan wannan ikirarin ba.

Mai magana da yawun fadar White House Ian Sams ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, "'Yan Republican a majalisar wakilai sun shafe watanni 9 suna binciken shugaban kasar, kuma ba su gano wata shaida ko hujja da ke nuna an aikata ba daidai ba."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG