Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga shugaban Amurka Joe Biden, da iyalan Albright, da kuma jami'an diflomasiyyar duniya, bisa rasuwar mace ta farko da ta rike mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka, Madeleine Albright.
An tuhumi wasu iyaye biyu da laifin kisan kai bayan da aka zarge su da barin diyarsu ta yi mummunar kiba a cewar jaridar The Telegraph.
Wani wakilin leken asiri na musamman, Andrew John Innocenti, dake aiki a karkashin hukumar binciken gwamnatin tarayya ta gwamnatin Amurka, ya yi zargin cewa fitaccen jarumin nan na Instagram Hushpuppi ya sake samun sabbin tuhume-tuhume.
An dakatar da Kanye West daga Instagram na tsawon sa'o'i 24 ne saboda keta manufofin dandalin kan kalaman ƙiyayya da cin zarafi, in ji mai magana da yawun Meta Laraba.
Yayin da hankalin duniya ya karkata a kan yaki tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, birnin New York a Amurka na daukar matakan kare al’ummarsa daga barazanar da cutar coronavirus ke yi a birnin da ya taba zama tungar annobar COVID-19 duniya.
Attoni Janar na Tarayya kuma ministan Shari'a Abubakar Malami ya mikawa Shugabar babbar kotun Tarayya takardar bukatar neman mikawa Amurkan DCP Abba Kyarin don fuskantar shari'a dangane da batun taka rawa a damfarar da ake zargin Hushpuppy da aikatawa.
Mazauna jihar New York sun gudanar da zanga zangar kin jinin harin da Rasha ta kai a kan Ukraine, yayin da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da sabbin takunkumai a kan Rasha.
Putin ne ya zabi shiga wannan yaki da kansa, saboda haka, shi da kasarsa za su girbi abin da suka shuka. Biden ya ce.
A ranar Litinin Putin ya Ayyana wasu yankunan Ukraine a zaman masu cin gashin kansu, wadanda ba sa karkashin kasar.
“Da ma mun yi tsammanin Rasha za ta dauki irin wannan mataki, kuma a shirye muke mu mayar da martini.” Sakatariyar watsa labarai a Fadar White House Jen Psaki ta ce a ranar Litinin.
Jami’an ‘yan sanda a jihar Florida da ke Amurka sun kama wani likitan jinyar gaggawa dan Najeriya mazaunin Amurka, mai suna Onyekachi Nwabuko dan shekaru 44 da haihuwa, sabili da cin zarafin marar lafiya.
Fitattun sojojin Amurka sun kashe shugaban kungiyar IS, a wani samame da suka kai cikin dare a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria, in ji shugaban kasar Joe Biden.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.