Abubakar Malami yace Najeriya ta dau wannan mataki ne biyo bayan bukatar da jami'an diflomasiyyar Amurka dake ofishin jakadancinta a Abuja suka mikawa Najeriya.
Najeriya inji Attoni Janar din ta amince da mika Abba Kyarin ne biyo bayan gamsuwa da cewa, batun bai da alaka da wani banbancin launin fata, addini, kasa ko ra'ayi, amma dai batu ne tsantsa dake da alaka da shari'a.
A hirar shi da Muyar Amurka, lauya da ke da kwarewa a tsarin mulki, Barrister Yakubu Sale Bawa ya bayyana cewa, ba haka kawai za a kai Abba Kyarin a mika shi ga Amurkan ba, sai kotun ta ga dacewar yin hakan.
Dangane kuma da batun da shari'ar da yake fuskanta a nan Najeriya kan batun safarar hodar Iblis, lauyan yace tunda batun shari'ar Amurkan ne ya fara kunno kai to yanzu ita za a fara, amma kuma za a iya ci gaba da batun shari'ar miyagun kwayoyinma a lokaci guda.
Masu fafutika a Najeriya irinsu Comrade Kabir Dakata na maraba lale da matakin gwnamnatin. Yana mai cewa magana ce ta shari'a. In yana da gaskiya, zai fidda kansa, in kuma yana da laifi, a mai hukunci.
Yanzu dai kallo ya koma babbar kotun Tarayya don ganin irin hukuncin da zata yanke akan wannan batu mai tsananin daurin kai da kuma ya dauki hankalin al'ummar Najeriya da ma wadansu kasashen duniya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: