Fitattun sojojin Amurka sun kashe shugaban kungiyar IS, a wani samame da suka kai cikin dare a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria, in ji shugaban kasar Joe Biden.
Yanzu dai ta tabbata cewa akwai sabon kyakkyawan fata ga ‘yan Najeriya dake son zuwa Amurka ganin yadda ofishin jakadancin Amurka ya ce zai kara bubbude kofofinsa wajen baiwa ‘yan Najeriya takardun izinin shiga kasar wato Visa
Daruruwan mutane daga sassa daban na gudandumar Bronx da ma New York da suka hada da Musulmi ne suka halarci sallar jana’iza.
Ana ci gaba da haɓaka allurar rigakafin COVID-19 a matsayin feshin hanci maimakon alluran hanu aƙalla dakin gwaje-gwaje tara da kamfanoni a duniya, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Shirin A Bari Ya Huce na wannan makon ya karrama tsohon shugaban Sashen Hausa Steve Lucas wanda Allah ya yi wa cikawa ranar Talata yana da shekaru 75 a duniya.
Kididdiga ta nuna cewa, kimanin mutum 44 ne suka ji rauni inda 13 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.
Likitoci sun yi famar ceto rayukan mutane da dama da suka samu munanan raunuka a ranar Litinin, lokacin da hayakin wuta ya buge su ko kuma ya makale da su a cikin gidajensu a wani babban bene na birnin New York. Mutane 19 da suka hada da yara 9 ne suka mutu a gobarar.
Masu zanga-zangar sun fito kan tituna a yammacin Turai don nuna adawa da buƙatun rigakafin COVID-19, tare da mutane sama da 100,000 da suka yi gangami a Faransa kaɗai don adawa da abin da suka kira shirin gwamnati na tauye haƙƙin waɗanda ba a yi musu allurar ba.
Yayin da ake samun karuwar satar mutane da sauran laifuka a Najeriya, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka tana kira ga Amurkawa da 'yan kasa biyu da sauran su da su "sake yin shawarar balaguro" zuwa kasar da ke yammacin Afirka.
Asibitoci a duk faɗin Amurka suna jinkirin aikin fida na tiyata don samar da isassun ma'aikata da gadaje saboda hauhawar cutar COVID-19 nau’in Omicron dake yaduwa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a duniya ya karu da kashi 11 cikin 100 a makon da ya gabata idan aka kwatanta da satin da ya wuce, inda nahiyoyin Amurka ne aka fi samun karin.
Hauhawar adadin masu kamuwa da cutar a Amurka ya sa wasu jami’o’i da dama sun ayyana shirinsu na yin karatu daga gida, cikinsu har da Jami’ar Havard.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.