Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shararriyar Mawakiyar Amurka Mary Wilson Ta Mutu


Mawakiya Mary Wilson
Mawakiya Mary Wilson

Wata shararriyar mawakiyar Amurka Mary Wilson da tayi fice a cikin fitattun mata mawaka uku da ake kira da The Supremes a cikin shekarun 1960 ta mutu tana da shekaru 76. 

Kawarta mai tallata fitattun mutane Jay Schwartz ta ce Wilson ta mutu farab daya ne a jiya Litinin a gidanta dake Las Vegas a jihar Nevada.

Wilson ita ce ta kafa kungiyar "The Supremes" tare da Diana Ross da kuma Florence Ballard yayin da suke zaune a gidajen jama’a a Detroit, a jihar Michigan a shekarar 1959.

Mawakan The Supremes
Mawakan The Supremes

Kungiyar ta kulla yarjejeniyar aiki da wani kamfanin shirya wakokin R&B na Motown Records bayan shekaru biyu amma wakarsu ta farko da ta shahara ita ce ta “Where Did Our Love Go” a shekarar 1964.

Shugaban kamfanin Motown Berry Gordy ya yabawa Wilson a cikin wata sanarwa a “matsayin fitacciyar taurari da ta san abin da take yi” wacce ta taka rawar gani shekaru da dama “domin daukaka kyakkyawar sunan The Supremes”

XS
SM
MD
LG