Rundunar sojojin Najeriya tayi karin haske kan yan kungiyarta da aka tarwatsa a jihar Nasarawa cewa tun watanni shida da suka gabata suka rikide zuwa Boko haram
Shugabannin Addini da Na Kungiyoyin Matasa Sun Kalli Majigin VOA Akan Boko Haram a Abuja.Wadanda suka kalli majigin sun hada da Shaikh Abdullahi Bala Lau shugaban IZALA da Rabaran Musa Asake, sakataren kungiyar kiristocin Najeriya.
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata dukufa wajen tabbatar da an sako sauran 'yan matan Chibok da duk wasu 'yan kasar dake hannun Boko Haram bayan da aka samu kubutar da 'yan matan 82.
Yayin da a Najeriya ake cigaba da maida martani game da ceto yan matan Chibok 82 da hukumomin kasar suka yi, yanzu haka wasu kungiyoyi da kuma al’ummomin da hare haren Boko Haram ya shafa na ganin akwai abun dubawa.
Baya ga 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace daga makarantarsu, kungiyar ta kashe tare da sace dubban mutane da suka hada da kashe da kuma kona makarantar sakandaren Buni Yadi da ma wasu dubban mata da yara
Hira ta musamman akan yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da amsoshin da kwamandan rundunar dake yaki da Boko Haram 2LT L.O Adeosun Ya ba wakilin Muryar Amurka N. Pinot
Shin ko kun san ainihin fuskokin ‘yan Boko Haram? Kamar yadda muka yi alkawarin gabatar maku, a cikin wannan bidiyo, wanda ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka dauka da hanunsu, za ku kalli fuskokin wasu daga cikin manyan shugabannin kungiyar.
Ranar 13 ga watan nan na Afirilu, Muryar Amurka zai saki wani bidiyo da zai nuna fuskokin manyan mayakan kungiyar Boko Haram a wani hoton bidiyo da suka da kansu, wanda ya mu shigo wa hanun Muryar Amurka. Ga somin tabi.
'Yan kunar-bakin-waken da ake kyautata zaton cewa 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan wasu sansanonin 'yan gudun hijira dake kusa da tashar motar Muna a Maiduguri, cikin daren da ya shige.
A lokacin da 'yan Boko Haram suke cin karensu babu babbaka, ga wani bidiyo nasu da ya nuna yadda suke sauke babura ko mashina a kofar gidan shugabansu a garin Kumshe sai dai ba a san inda suka samo wadannan babura ko mashina ba, wadanda sabbi ne ful a cikin kwalayensu.
A wannan bidiyo, Khalifa Aliyu Ahmad Abulfathi zai yi bayani kan mummunar akidar kungiyar Boko Haram da irin ta’asar da suka yi a lokacin suna ganiyar kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.
A wannan bidiyo za ku kalli yadda ‘yan kungiyar Boko Haram suke gudanar da atusaye da motsa jiki a wani yankin arewa maso gabashin Najeriya da suka karbe ikonsa a lokacin suna ganiyar cin karensu ba babbaka a tsakanin shekarun 2014 da 2015. A yi kallo lafiya.
Domin Kari