Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Tayi Karin Haske Kan Yan Kungiyarta Ta Tarwatsa a Nasarawa


Major General M.G Ali
Major General M.G Ali

Rundunar sojojin Najeriya tayi karin haske kan yan kungiyarta da aka tarwatsa a jihar Nasarawa cewa tun watanni shida da suka gabata suka rikide zuwa Boko haram

Ana kara samun haske kan 'yan kungiyar ta'addar nan da aka tarwatsa a jihar Nasarawa da ke arewa maso tsakiyar Najeriya.

Kwamandan sojoji na musamman dake garin Doma a jihar Nasarawa, Manjo Janaral M.G.Ali ya shaidawa Muryar Amurka cewa tun watanni takwas da suka wuce kungiyar ta rikide zuwa ta Boko Haram.

Janaral Ali yace suna da bayanan sirri cewa a baya jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau ya tura wakilinsa zuwa ga Darussalam inda ya nemi su karbi akidar Boko Haram.

Ko da suka ki yarda, mayakan Shekau din sun yi wa jagororin na Darussalam kisan gilla inda suka amshe jagorancin sansanin. Kafin daga bisani sojoji na musamman din suka tarwatsa su.

Amma Ohinoyi na Dausu, Alhaji Idriss Hakimin Dausu dake Kasar Toto ya shaidawa Muryar Amuka cewa har yanzu fa akwai sauran yan wannan kungiya a yankunan su.

Domin a halin yanzu basu isa suje gonakinsu ba, don sai a yi garkuwa dasu har sai an biya makudan kudi.

'Yan asalin jihar Nasarawa irinsu Alhaji Mohammed Lawan, Sardauna na mai cewa akwai sauran wurare irin Nasarawa da Loko da namma akwai sauran 'yan ta'addannar. Don haka akwai bukatar gwamnati ta kara jan damara sosai don tunkarar matsalar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Nasarawa Mr. Dogo Shamman yace za a maida iyalan wadanda aka tarwatsa din ga gwamnatocin jihohinsu na asali daban, su kuma 'yan asalin jihar za a tattara su wuri guda kafin a san yadda za a yi dasu.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG