Tun da aka ceto da kuma musayar Yan matan Chibok 82,masana da kuma kungiyoyi a Najeriya ke bayyana ra’ayinsu inda wasu ma ke ganin akwai abun dubawa ganin cewa kawo yanzu akwai wasu da dama da ke hannun yan bindigan masu tada kayar baya.
Manazarta irinsu Abdullahi Damare na kungiyar Shiga Tsakanin Musulmi da Kirista ta Interfaith Mediation Centre,na ganin ya kamata gwamnati ta fadada wannan yunkuri na musayar ya hada da wasu da aka kama kafin ‘yan matan Chibok da kuma bayan an sacesu .
Bayanai na nuni da cewa , akwai daruruwan wasu dake hannun mayakan na Boko Haram wadanda ba’a san halin da suke ciki ba, batun da dan majalisar wakilai Mr Adamu Kamale ke cewa suma a duba batun jama’arsu da aka sace.
Kawo yanzu hankula sun fara kwantawa a wasu yankunan da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram. To ko yaya al’umman wadannan yankuna ke ji da musayar da aka yi ayanzu? Mallam Yakubu Musa wani dan asalin yankin Uba ,ya bayyana farin cikinsu kamar haka.
Rahottani sunce kungiyar bada agaji ta Red Cross da gwamnatin kasar Switzerland ne suka jagoranci tattaunawar da ta kai aka sako ‘yan matan.Kuma tun a watan Afrilun 2014 ne dai mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da ‘yan matan su fiye da 270 daga makarantar sakandare dake garin Chibok a jihar Borno.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum