Kawo yanzu babu wani labari daga 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sako saboda har yanzu gwamnati tana rike dasu a wasu wurare.
Alkalumma sun nuna 'yan mata dari biyu da saba'in da shida ne 'yan Boko Haram suka sace tun farko, hamsin da bakwai kuma suka kubuta, aka tsinto uku kana aka sako dari da uku ta hanyar yarjejeniya.
Yanzu ana neman saura dari da goma sha uku da ake kyautata zaton watakila wasunsu suna raye ko kuwa akwai wani lamari akasin hakan.
Aisha Yusuf ta kungiyar BBOG, kungiyar dake fafutikar neman an kubutar da 'yan matan Chibok tace bata taba ganawa da 'yan matan ba. Tace suna bukatar kula ta musamman kafin su koma gidajensu. Tana mai cewa suna son su taimaka idan an bari sun gansu. Saidai ko ba'a barsu su gansu ba yakamata a bar iyayensu su gansu.
A nasu bangaren daya daga cikin iyayen da 'yan Boko Haram suka kashe 'ya'yansu a makarantar sakandaren Buni Yadi Ado Malam Madalla na ganin yakamata a gayawa 'yan BBOG cewa banda 'yan matan Chibok akwai irin iyayen 'yan matan Chibok sun fi dari uku da 'yan Boko Haram suka tafi dasu. Babu labarinsu har yanzu.
Malam Madalla yace a makarantar Buni Yadi an kashe yara sun fi dari. Yace a kofar gidansa aka yiwa dansa harbi sau tara. Yace an debi matansu har ma duk wadan suke gidan mai anguwansu aka kwashe aka yi gaba dasu a Buni Yadi. Yace babu wanda ya tuna da Buni Yadi ko ya zo yayi zanga zanga.
Kwamitin shugaban kasa dake kula da arewa maso gabas yace abun da ya sanya gaba shi ne tsugunar da mutanen da 'yan Boko Haram suka rabasu da muhallansu.
Alhaji Tijjani Tumsa mataimakin shugaban kwamitin yace yadda sojojin kasar suka kwato wuraren to yanzu hakkinsu ne su tabbatar al'ummar wuraren sun koma matsugunansu. Dalili ke nan da Shugaba Muhammad Buhari ya nada kwamiti dinsu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum