A Nijar sakamakon farko farko na zaben shugaban kasa, ya nuna shugaba Muhammadou Issoufou yana kan gaba, amma tuni 'yan hamayya suka yi watsi da sakamakon zaben.
Kusa a cikin kawancen jam'iyyun adawa Ahmadu Bubakar Sise ya zargi hukumar zabe da taimakawa jam'yyar dake mulki wurin yin aringizon kuri'u domin cimma burin cin zabe a zagayen farko kamar yadda shugaban kasar ya yi ikirari
An fara kirga kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da aka gudanar a jamhuriyar Nijar bayan rufe runfunan zabe jiya Lahadi. Mai yiwuwa ba za a fitar da sakamakon zaben ba sai mako mai zuwa.
Yayin da hukumar zaben kasar Nijar ke tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar Dokokin da aka gudanar jiya Lahadi, masu sa ido na kungiyar tarayyar Afirka sun yabawa halin dattakon da ‘yan kasar ta Nijar suka nuna inda komai ya kammala ba tare da wani hargitsi ba.
Jami’an zaben jamhuriyar Nijar a babban birnin tarayya Abuja, sun ayyana dan takarar MODEN LUMANA, Hama Amadou a matsayin wanda ya sami nasara, shugaba Muhamadou Issoufou na PNDS TARAYYA na dafa masa baya, sai kuma Seyni Oumarou na MNSD NASSARA ya zo na Uku.
ZABE A NIJAR: Daga dakin yada labaru sashen Hausa na muryar Amurka a lokacin da yake gabatar da shirinsa na karfe 9:30 agogon Najeriya da Nijar akan zaben shugaban kasa da 'yan majalisun jamhuriyar Nijar
Wannan shine karo na 6 da ake shirya babban zabe a Jamhuriyar Nijar, tun bayan da kasar ta tsunduma tafarkin dimokaradiyya a 1991, lokacin da kungiyoyin fafutukar kasar suka kawo karshen mulkin shekaru 16 da Janal Ali Saibou ya gada daga marigayi Janal Seyni Kountché.
Yayin da yan kasar Nijar da dama ke zaune a Najeriya, musammam a makwabtan jihohi irin su Sokoto da Kebbi da Zamfara, suka koma gida domin gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisar Dokoki, wasu da yawa suna jiran jefa nasu kuri’un a Najeriya.
Domin Kari