Sakamakon kidayar da hukumar zaben kasar ta bayyana a safiyar yau Talata, ya nuna shugaba Isouffou yana kan gaba da kimanin kashi 40 cikin dari na kuri'un da aka kada, yayinda dan hamayya Hama Amadou yana da kashi 29 cikin dari, sai kuma Seyni Oumaru yana da kashi 12 cikin dari.
Sakamakon zaben ya shafi gundumomin zabe 20 ne daga cikin gundumomi 308 na kasar.
Gamayyar jam'iyun hamayya tuni ta yi watsi da sakamakon da cewa magudi ne aka yi. Shugaban gamayyar ta 'yan hamayya, Amdou Cisse, ya fada yau talata cewa, gwamnati ta kafa "dubban rumfunan zabe na karya"domin ta murda sakamakon zaben.
Shugaba Muhammadu Isouffou, yana neman wa'adi na biyu wasu shekaru biyar, tareda alkawarin zai murkushe mayakan sakai masu ikirarin musulunci, sannan ya habaka kasar Nijar, wacce take cikin jerin kasashe mafiya talauci.