An fara kirga kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da aka gudanar a jamhuriyar Nijar bayan rufe runfunan zabe jiya Lahadi. Mai yiwuwa ba za a fitar da sakamakon zaben ba sai mako mai zuwa.
Yayin da hukumar zaben kasar Nijar ke tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar Dokokin da aka gudanar jiya Lahadi, masu sa ido na kungiyar tarayyar Afirka sun yabawa halin dattakon da ‘yan kasar ta Nijar suka nuna inda komai ya kammala ba tare da wani hargitsi ba.
Jami’an zaben jamhuriyar Nijar a babban birnin tarayya Abuja, sun ayyana dan takarar MODEN LUMANA, Hama Amadou a matsayin wanda ya sami nasara, shugaba Muhamadou Issoufou na PNDS TARAYYA na dafa masa baya, sai kuma Seyni Oumarou na MNSD NASSARA ya zo na Uku.
ZABE A NIJAR: Daga dakin yada labaru sashen Hausa na muryar Amurka a lokacin da yake gabatar da shirinsa na karfe 9:30 agogon Najeriya da Nijar akan zaben shugaban kasa da 'yan majalisun jamhuriyar Nijar
Wannan shine karo na 6 da ake shirya babban zabe a Jamhuriyar Nijar, tun bayan da kasar ta tsunduma tafarkin dimokaradiyya a 1991, lokacin da kungiyoyin fafutukar kasar suka kawo karshen mulkin shekaru 16 da Janal Ali Saibou ya gada daga marigayi Janal Seyni Kountché.
Yayin da yan kasar Nijar da dama ke zaune a Najeriya, musammam a makwabtan jihohi irin su Sokoto da Kebbi da Zamfara, suka koma gida domin gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisar Dokoki, wasu da yawa suna jiran jefa nasu kuri’un a Najeriya.
Babban taron muhawara na kasa da ake kira conférence nationale, na ranar 29 ga watan Yuli na shekara ta 1991, shine ya bada damar girkuwar tafarkin dimokaradiyya a jamhuriyar Nijar, wanda hakan ya bada damar bayyanar jam’iyyun siyasa daban daban.
A ranar 21 ga watan Fabarairu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko hade da na 'yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar, za kuma gudanar da zagaye na biyu a ranar 28 Maris.
Domin Kari