A shekaru 25 da gudanar da wannan babban taron muhawara na kasa, jamhuriyar Nijar ta samu shirya zabuka daban daban har guda 5, wannan zaben da za a gudanar yau 21 ga watan Fabarairu ya kasance na 6 da jamhuriyar Nijar ta shirya a tarihin zabe.
Koya ake kallon tafarkin dimokaradiya a shekaru 25 din da suka gabata? Tambayar kenan da wakilin Muryar Amurka a Nijar Yusuf Abdoulaye, ya yi wa Alhaji Issoufou Bashar tsohon jami’in difilomasiya a Nijar.
Alhaji Issoufou, yace yanzu siyasa ta kara lalacewa a jamhuriyar Nijar, domin yanzu ba a amfani da ra’ayi sai dai a saya da kudi, wanda hakan shike ci wa mutane tuwo a kwarya.
Wannan zaben na da matukar muhimmamcin gaske domin ya kasance zabe na biyu da wani farar hula ya shirya bayan ya kammala wa’adinsa na farko. Wani abu kuma da ake ganin yana da muhimmamci a zaben shine samun yan takara da yawa a bangaren matasa, kama tun daga takarar yan majalisar Dokoki zuwa na shugaban Kasa.
Yan takarar neman shugabancin Kasa 15 ke fafatawa a zaben na yau, san nan 5200 a bangaren yan majalisar Dokoki.