Likitar yar takarar shugaban kasa a jami’iyar Democrat Hillary Clinton tace Hillary din tana samun lafiya sosai daga ciwon hakarkari da ya cafke ta kuma tana jin karfin jiki da zata iya jan ragamar shugabancin Amurka.
'Yar takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar democrats ta Amurka, Hilary Clinto, ba zata yi kyamfen yau Litinin ko gobe Talata ba a jihar California bayanda likitoci suka tabattarda cewa tana fama da ciyon harakari.
‘Yar takarar shugabancin Amurka ta jam’iyar Democrat Hillary Clinton tace, abu mafi muhimmanci ga kowane shugaban kasa shine ya kasance mai natsuwa. Yayinda abokin hamayyarta na jam’iyar Republican Donald Trump yace, kada irin halinsa da tunaninsa su dami masu kada kuri'a.
Dan takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Republican Donald Trump ya matso dab da abokiyar karawarsa ta jam’iyyar Democrat Hillary Clinton a sakamakon zaben jin ra’ayin jama’a, makonni uku kafin ‘yan takarar su hadu da juna a dandalin muhawara.
Dan takarar Shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya fadi jiya Laraba cewa a gwamnatinsa, babu yadda za a yi wadanda su ka shigo Amurka a sace su zama 'yan kasa.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Republican Donald Trump zai gana da shugaban kasar Mexico Entrique Pena Nieto yau Laraba, kafin jawabin da zai gabatar inda zai bayyana tsare tsarensa na shige da fice.
Sama da mako guda kenan ‘dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Donald Trump, ya yi ta zargin abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton, da nuna wariyar launin fata da rashin mutunta ra’ayin jama’a,
A karo na biyu cikin wannan makon, wasu kungiyoyi na jam’iyyar Republican ta Amurka, sunce ba zasu goyi bayan Donald Trump ba a matsayin dan takarar shugaban ‘kasa.
’Yar takarar shugabancin Amurka karkashin tutar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton jiya laraba ta roki 'yan jam'iyyar Republican dama masu indifanda da su jefa mata kuria.
Shugaban Amurka Barack Obama yace doka ta umarci gwamnatinsa da ta bayar da bayanan sirri, ciki har da wanda aka sakaya ga ‘yan takarar shugabancin kasar.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump wanda ya kwashe sati guda yana cece kuce akan batun Khizr da Ghazala Khan, iyayen wani sojan Amurka da aka kashe a Iraqi, ya janyo wasu ‘yan jamiyyar tasu ta Republican fitowa fili suna sukar dan takarar nasu.
Caccakar da dan takarar shugaban kasar Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya ke sha, ta kara tsanani jiya Talata, saboda sukar wani iyalin Musulmin Amurka wadanda dan su ya mutu yayin da ya ke yaki ma Amurka a Iraki a 2004.
Domin Kari