Sama da mutane 70 ‘yan jam’iyyar, cikin harda tsohon ‘dan majalisa da tsoffin shugabannin Majalisar lokacin mulkin shugaba Reagan da shugaba Bush ‘karami da babba, sun aika da wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar Reince Priebus.
Suna bukatar jam’iyyar da dakatar da yin amfani da kudadenta da lokacinta da yin tallace tallacen neman a zabi Trump, maimakon haka tayi amfani da su akan ‘yan Majalisun Dokoki da na Wakilai. Sunce yiwuwar Trump ya samu nasara a zaben watan Nuwamba na ‘kara dusashewa a kullu yawmin.
Cikin dalilan da sukayi amfani da shi akwai na maganar kace nace da baban tsohon sojan nan da aka kashe a Iraqi.
Jami’in sadarwa na jam’iyyar Republican Andrew Weinstein, ya fadawa Muryar Amurka cewa, idan har jam’iyyar bata canza alkiblarta ba, to tabbas zaben watan Nuwanba Trump ka iya zuguza rinjayen da jam’iyyar ake da shi a Majalisun Amurka.
Har yanzu dai Trump bai mayar da martani ba kan wannan magana.