Dayawa zaben jin ra’ayin jama’a na nuna yadda tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillari Clinton, ta ke gaba da Trump, shararren ‘dan kasuwar nan mai sayar da gidaje wanda yake wannan shine karonsa na farko a tsayawa takara.
Amma yanzu haka ya kusa kamo tazarar da ta bashi da kaso 4 cikin 100, wato yanzu haka ya kamo rabin tazarar da ta bashi makonni kadan baya. Duk kuwa da cewa tana ci gaba da zama gaban Trump a kowane fanni, wanda ke ganin hakan ka iya nuna yadda zaben da za a gudanar 8 ga watan Nuwamba mai zuwa zai kasance.
Masana harkar siyasa a nan Amurka har yanzu suna harsashen cewa Hillary ce zata zamanto shugabar kasar Amurka ta 45, kuma mace ta farko da ta taba samun wannan matsayin, don maye gurbin shugaba Obama lokacin da zai bar ofis a watan Janairun shekara mai zuwa. Amma masanan sun ‘dan rage hangensu cikin ‘yan kwanakin nan.