A siyasar Amurka 'yan takara kowace jam'iyya sai sun yi watanni suna muhawara tsakaninsu da nufin tallata kansu kafin su tsaya takarar fidda gwani da zai zama wakilin jam'iyyarsu da zai fafata da duk wanda jam'iyyar Democrat ta tsayar
Shugaban Amurka Barack Obama na shirin yin anfani da ikon da dokar kasar ta bashi na matakin tsatsaura yadda mutane ke sayen bindigogi.
Hamshakin attajirin nan na Amurka Donald Trump, ya tasamma sabuwar shekara da gagarumar rinjaye tsakanin abokanan takararsa karkashin jam'iyyar Republican.
‘Yan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam’iyar Republican su tara, sun karkata hankulansu akan batun tsaro da ayyukan ta’addanci, yayin da suke yin muhawararsu ta biyar a daren jiya Talata.
Sakamakon neman jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan ya nuna cewa babu abunda Donald Trump zai fada zuwa yanzu da yake illa ga matsayinsa na zaman kan gaba a wajen masu ra'ayin mazan jiya wadanda suke goyon bayansa, Kasa da wata biyu kamin a fara jefa kuri'arzaben fidda dan takara da ake farawa daga jihar Iowa, a cikin watan biyu.
Mutane 10 da suke neman jam'iyyar Republican tana nan Amurka ta tsaida takarar shugabancin Amurka sun kara kan manufofinsu kan tattalin arziki da kuma sukar junansu a muhawara ta uku da suka gudanar a daren jiya Laraba.
Lokacin siyasa 'yan takara sukan fadi wasu abubuwa da yawa. A nan Amurka an samu wani dan takara dake ganin shugabanin Afirka basu iya mulki ba saboda haka a sake yi masu mulkin mallaka na shekaru dari.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump yace yau da duniya tana zaune lafiya inda 'yan mulkin kama karya su Saddam Hussein, da Moammar Gadhafi suna kan mulki. Jiya Lahadi ne Trump ya furta a magana da yayi da wasu kafofin yada labarai.
Yanzu haka tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta soma gabatarda bayanai a gaban wani kwamitin musamman na ‘yanmajalisar dokokin Amurka.
Bayan da masu takararar neman Jam'iyyar Republican ta tsaida su takarar shugabancin Amurka da suka kara har sau biyu,takwarorinsu a bangaren Jam'iyyar Democrat sunyi tasu muhawara ta farko saboda zaben shugaban kasa da za'a yi badi. Sun gwabza ne a birnin Las Vegas a daren jiya Talata.
Kamar yadda siyasar Amurka take duk mai neman wani mukami wala na zama dan majalisa ko gwamna ko shugaban kasa sai ya tallatar da kansa ta hanyoyi daban daban da doka ta tanada kana ya tsaya zaben fidda gwani na jam'iyyarsa kafin ya tsaya takara.
Tun bayan da ta bayyana aniyar ta sake tsayawa neman takarar shugabancin kasar Amurka, tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen kasar, a yau Asabar Hillary Clinton ta yi wani gangami mafi girma a birnin New York.
Domin Kari