A yau Litnin Shugaban Amurka Barack Obama, zai gana da manyan jami’an tsaron kasar, gabanin ayyana damar da doka ta bashi, da zai kara tsaurara matakan mallakar bindiga a karkashin dokokin tarayyar kasar.
Obama ya gayyaci Attorney Janar Loretta Lynch da Darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, James Comey da sauran manyan jami’an tsaro zuwa Fadar White House, domin tattaunawa kan irin matakan da ya kamata ya dauka wajen dakile kashe-kashen da ake yi da bindiga a kasar.
Idan dai har zai yi amfani da karfin ikon da doka ta bashi na gashin kansa, shugaba Obama ba ya bukatar iznin majalisar dokokin kasar, wacce ke karkashin jagorancin ‘yan jam’iyyar Republican, wadanda ke adawa da matakin da Obama ya ke so ya dauka kan mallakar bindiga.
Wannan mataki da Shugaban Amurkan ke so ya dauka na zuwa ne bayan jerin kashe-kashen da aka samu a kasar ta Amurka a