Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Siaysar Amurka Na Kiran A Sake Yiwa Afirka Mulkin Mallaka


Wasu cikin 'yan siyasan Amurka Donald Trump a hagu da Jeb Bush a dama dukansu 'yan jam'iyyar Republican
Wasu cikin 'yan siyasan Amurka Donald Trump a hagu da Jeb Bush a dama dukansu 'yan jam'iyyar Republican

Lokacin siyasa 'yan takara sukan fadi wasu abubuwa da yawa. A nan Amurka an samu wani dan takara dake ganin shugabanin Afirka basu iya mulki ba saboda haka a sake yi masu mulkin mallaka na shekaru dari.

'Yan siyasan suna cewa 'yan Afirka basu iya komi ba illa su saci kudin kasashensu kana su turasu zuwa turai su yi gaban kansu dasu.

A cewar dan siyasar kamata ya yi a sake yiwa nahiyar mulkin mallaka na akalla shekaru dari saboda wai, basu iya tafiyar da al'ummarsu ba.

Akan wannan batun ne Muryar Amurka ta tattauna da Dr Isyaka Alhassan Kauranmata na kwalagin kimiya dake Kaduna.

Dr Isyaku yace maganar dadaddiya ce. Ko kafin furucin baya bayan nan da yawa cikin turawa basu dauki bakaken fata mutane ba. Akwai wadanda suke ganin bakin fata kamata ya yi ya cigaba da zama bawa.

Dr. Isyaku yace akwai kanshin gaskiya a maganarsu cewa baki bai iya shugabanci ba. Yace akwai kanshin gaskiya domin an samu shugabanni a wurare daban daban da suka yi barna, suka kwashe dukiya suka kai turai suka jibge. Turawan suna anfani da dukiyoyin suna gina turai, suna samun bunkasar arziki da cigaba da walwala bayan kuma ita Afirkan tana fama da talauci.

Satar da shugabanninmu ke tana kara masu karfin gwuiwar cewa Afirka bata san abun da ta keyi ba.

A bangare daya gaskiya ce akwai matsaloli na shugabanci da irin tunanen mutanen Afirka. A kasashen Afirka da dama da suka hada da Najeriya an samu mutane sun kwashe kudin kasa sun fita waje dasu. Yanzu abun da Najeriya take fama dashi shi ne yadda za'a dawo da kudaden.

Batun cewa a mayarda Afirka mulkin mallaka tana yiwuwa wanda ya yi maganar bai san tarihi ba ko kuma yana kokarin juya tarihi ne. Mulkin mallaka ba alheri ba ne garesu da Afirka kanta saboda ba taimako suka zo yi ba sun zo ne su kama bayi, su sace kasa su kuma sace dukiyarta da kuma yin anfani da dukiyar Afirka wajen gina tasu kasar.

Kada a manta dole ne ya sa suka kawo karshen mulkin mallaka domin idanun mutane sun waye. Mutane sun tashi ba zasu cigaba da zama masu bauta ba dole ne a basu kasarsu. Da zasu tafi mutanen suka zama 'yan amshin shatansu suka ba shugabanci. Kuma yawancin matsalolin Afirka turawan mulkin mallaka suka dasasu.

Maganar a sake yiwa Afirka mulkin mallaka maganar banza ce domin ba wai suna tunanen su yi abun da ya dace ba ne, wato su gyara mutanen Afirka.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:00 0:00

XS
SM
MD
LG