Tun lokacin da cutar ebola ta bulla gwamnatoci kama daga kananan hukumomi zuwa tarayya suke iya bakin kokarinsu domin ganin cewa mutane basu kamu da cutar ba domin ko likitoci sun tabbatar cewa cikin kashi goma na wadanda suka kamu da cutar da kyar hudu ke warkewa,sauran mutuwa su keyi.
Ministan ilimin Najeriya Malam Ibrahim Shakarau ya karanta bayanin tsawaita hutun makarantun firamare da sakandare da makonni shida a duk fadin kasar domin a haras da malamai akan yadda zasu binciki yaran makarantunsu su gano masu dauke da kwayar cutar ebola.
Gwamnatoci, daga kananan hukumomi, zuwa na taraiya na kokari domin ganin cewa mutane basu kamu da cutar Ebola ba.
Ganin yadda jihar Borno ke makwaftaka da kasashen Afirka uku yasa uwargidan gwamnan Borno ya sa Hajiya Nana Kashim Shettima ta shirya taron fadakar da kawunan jama'a akan cutar ebola
Wakilin jakadan Saudiya a Abuja ya tabbatar cewa zasu fara ba 'yan Najeriya maniyattan bana takardar zuwa hajji daga yau ko gobe.
Yankin Maigatari, na jiran kayyakin aiki dangane da kariyan Ebola.
Biyo bayan killace inda wasu suka abkawa wurin da aka kebe masu fama da cutar ebola da jami'an tsaro suka yi yanzu kura ta lafa
Kayayyaki har sun fara hau-hawa a Kamaru sanadiyar rufe kan iyakoki.
Sabanin maganganun da a keyi na cewa cutar ebola cuta ce da idan an kamu da ita ba makawa sai mutuwa amma batun ba haka yake ba domin mutane biyar cikin wadanda suka kamu da cutar sun mike kuma likitoci sun tabbatar basu dauke da kwayar cutar a jikinsu yanzu.
Karamar hukumar kuje a shake da jama’a masamman ma’aikata dake aiki cikin babban birnin taraiya
Domin Kari