Manufar taron shi ne kare yaduwar cutar a kasar musamman a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.
Gidauniyar uwargidan gwamnan ta gayyato kungiyoyi masu zaman kansu ne har su arba'in da takwas tare da kwararun likitoci domin su fadakar da al'umma kan illar cutar ebola da kuma hanyoyin da za'a bi domin kaucewa kamuwa da cutar.
Alhaji Zanna Mustapha mataimakin gwamnan shi ya bude taron. Ya kuma jawo hankulan mutane akan cutar da yace su basu santa ba cuta ce da ta samo asali daga cin namun daji. Idan ba'a ci namun daji ba ba'a kuma yi muamala da wanda ya kamu da ita ba to an tsira.
Likita Fatima Jamil tace kada jama'a su tsorata da cutar . Hasken rana ma na kashe kwayar cutar. Anfani da sabulu ko toka duk suna kashe kwayoyin. Duk lokacin da aka yi anfani da wasu abubuwa a yi kokari a wanke hannaye. A gujewa gaisawa da mutane barkatai da cin naman birai ko kuma na jemaje. Ta hanyar jini da yawu da maniyi da gumi ko kuma ruwan da ya fito a jikin mutum duk hanyoyi ne na iya kamuwa da cutar.
Alhaji Muhammed Bello shugaban gidauniyar uwargidan gwamnan yace ita ce tace maza cikin gaggawa a fadakar da mutane akan cutar tunda suna da likitoci wadanda kuma zasu kula da mutane kayauta.
Sheikh Murtala Abdulfatahi yayi bayani akan yaduwar cututtuka inda yace a musulunci lafiya ita ce komi. Idan babu ita ba abun da za'a iya yi. Babban abun da mutun zai yi shi ne ya nemi lafiya dalili kenan tsafta da lafiya suke kafada da kafada.
Ga karin bayani daga Haruna Dauda Biu.