Sanarwar ta kwantar da fargabar dakatar da 'yan Najeriya daga aikin hajjin bana biyo bayan shigowar cutar ebola.
Uba Mana jami'in labaru ta hukumar alhazan Najeriya yace maganar dakatar da Najeriya daga aikin hajjin bana bata ma taso ba domin duk wani abun da yakamata Najeriya tayi ta dakile cutar ebola tayi. To sai dai idan lokacin zuwa hajjin yayi kuma aka ga wani da alamar cutar to ba za'a bari ya tafi ba.
Sakataren alhazan Gome Usman Gurama a taron masu ruwa da tsaki a aikin hajjin yace sun shirya tsaf domin tafiya aikin hajjin. Sun tara alhazansu baki daya wajen da ake yi masu bita kuma an yi masu bayanai ga yadda cutar take da yadda za'a maganceta. Da ma can su basu yi zaton za'a ma dakatar da Najeriya ba.
Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya yiwa maniyattan nasiha. Yace duk wanda zai tafi aikin hajji ya tabbatar cewa kudin da zai yi anfani dashi domin zuwa aikin hajji kudi ne na halal. Kudin da aka tanada domin aikin hajjin idan ba na halal ba ne Allah ba zai karbi aikin ba.
Haka kuma Sheikh Nasiru Abdulmunmuni yace malamai a shirye suke domin fadakar da alhazan. Hukumar alhazai ta kasa ta yadda cewa duk malaman dake karantaswa a hukumarta su karantar da jihohin da suka dace suna da bukata.
Za'a fara jigilar alhazan ranar shida ga watan gobe daga sabon filin jirgin saman Dutse dake jihar Jigawa. Haka kuma a karo na farko kamfanin Saudiya zai shiga jigilar alhazan Najeriya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.