An ba da rahoton samun kwanciyar hankali amma tare da zaman dardar a unguwar West Point ta Monrovia, babban birnin kasar Liberia, kwana guda bayan da 'yan sandan kwantar da tarzoma su ka fafata da mazauna wurin, wadanda su ka yi yinkurin bude wani wurin da aka killace don dakile yaduwar cutar Ebola.
Mutune akalla hudu sun sami raunuka ranar Laraba bayan da 'yan sanda su ka bude wuta tare da harba barkwanon tsohuwa don su kori masu zanga-zangar da ke jefa da duwatsu, wadanda su ka fusata saboda katse hanyoyin shiga da kuma fita unguwar.
A halin da ake ciki kuma, wasu Amurkawa biyu 'yan aikin agaji da su ka kamu da cutar ta Ebola a Liberia sun warke kuma har an sallame su daga wani asibitin birnin Atlanta da ke kudancin Amurka.
An yi jinyar Kent Brantly da Nancy Writebol a Asibitin Koyarwa Na Jami'ar Emory da magungunan da su ka hada da na gwaji, wanda ake kira ZMapp. Su ne na farkon samun wannan maganin, kuma likitoci ba su san ko shi ne ya taimaka masu wajen warkewa ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cutar Ebola ta kashe mutane 1,350 a Yammacin Afirka, kuma 576 daga cikinsu daga Liberia su ka fito.