Albarkacin cikon shekara daya da sace 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka yi a arewacin Najeriya, Muryar Amurka za ta shirya wata muhawara tsakanin kwararrun masanan da za su tattauna batun sace 'yan matan, da kuma kalubalen kubutar da 'yan matan dake hannun 'yan Boko Haram har yanzu.
Ba Mu Manta Da 'Yan Matan Chibok Ba
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar boko haram ne, suka shiga wata makarantar sakandare a garin Chibok dake jihar Borno suka sace wasu ‘yan mata guda 276.
Masu zanga-zangar lumana sunyi kira ga Gwamnati da ta ceto ;yan matan da aka sace daga makaranta ya'u shekara daya kennan, a Abuja Najeriya, Litinin 13, ga Afirilu 2015. Kusan 'yan mata dari uku ne aka sace wasu daga cikin sun samu sun kubuta da kansu.
Yau shekara daya ke nan cur da 'yan Boko Haram suka sace daliban makarantar 'yan mata a garin Chibok jihar Borno.
Duk da cewa yankuna da dama ya komo hanun dakarun Najeriya a fadan da su ke yi da Boko Haram, hukumomi sun ce har yanzu babu duriyar 'yan matan Chibok.
Bayanai daga hukumomin tsaron Najeriya na nuna cewa sun sami nasarar kwato garin Bama dake jihar Borno daga hannun maharan da ake kyautata zaton ‘yan boko haram ne, garin da suka kame fiye da watanni 7 da suka wuce.
Bayan kaddamar da wani hari da su ka yi a ranar Lahadin da ta gabata, dakarun hadin gwiwa daga kasashen Chadi da Nijar sun yi nasarar kwato garin Damasak da ke Najeriya.
Iyayen 'yan matan Chibok da a ka sace sun maida martani ga gwamnati inda su ka ce sun gaji da gafara sa kuma ko kaho ba sa gani.
Domin Kari