Iyayen dalibai mata fiye da dari biyu da ‘yan bindiga suka sace a makaranta a garin Chibok har yanzu ba’a gansu ba bayan mako daya,duk da kokarin da jami’an tsaro da wasu iyayen yaran suka yi na binsu cikin mugun daji.Wasu daga cikin daliban su tsira da tsalle daga mota ko kuma boyewa a cikin daji.
Hotunan Makarantar Sakandare na Chibok, an Dauka 21 ga Afrilu 2014

1
Gwamna jihar Borno Kashim Shettima, a tsakiya lokaci da ya kai ziyara makarantar sakandare na Chibok.An dauki hoton nan 21 ga Afrilu 2014.

2
Dalibai mata su hudu na makarantar sakandare na Chibok,a cikin wanna hoton da aka dauka 21 ga Afrilu 2014.

3
Jami’an tsaro sun wuce ta gaban makarantar sakandare na Chibok,inda ‘yan bindiga suka sace fiye da dalibai dari biyu.An dauki hoton nan 21 ga Afrilu 2014.

4
Gungun mutane na kallon makarantar sakandaren gwamnati na Chibok inda ‘yan bindiga suka sace fiye da dalibai dari biyu a Chibok,Najeriya. An dauka hoto 21 ga Afrilu 2014.