Kwana bayan girke jami’an sojin Amurka a Chadi, tuni sun fara aika jirage marasa matuka a ciki domin neman daliban nan mata sama da 250 da ‘yan Boko Haram suka sace.
Hadakar kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta nemi mahukunta su dinga horas da 'yan kungiyarta domin inganta harkokin tsaro a kasar.
A firarsa da wakilin Muryar Amurka gwamnan Borno yayi imanin za'a kwato yaran da aka sace tare da kokarin jami'an tsaro hade da taimakon jami'an tsaron kasashen waje.
A cigaba da kiraye-kirayen sako daliban Chibok da 'yan Boko Haram suka sace kungiyar matan kirista ko CAN ta arewa maso gabas tayi gangami da kiran a sako daliban Chibok a kuma daina hallakasu
Biyo bayan sace 'yan matan sakandaren Chibok da kungiyar Boko Haram tayi da cigaba da tabarbarewar tsaro gwamnati ta kwashe 'yanmatan sakandaren tarayya dake Monguno zuwa ta Maiduguri inda akwai ingantaccen tsaro kana kuma su cigaba da karatunsu.
Tsawaita dokar tabaci da gwamnatin taraiya tayi a jihojin arewa maso gabashin Najeriya yayi kyau domin kara tsaro a yankin.
Yayin da ake zaton za'a shawo kan 'yan Boko Haram masu haddasa ta'adanci sai gashi wasu bamabamai sun tarwatse a tsakiyar birnin Jos fadar gwamnatin jihar Filato.
Kasashen dake makwabtaka da Najeriya sunyi alkawarin bada bataliya guda-guda na hadin gwiwa domin tsare yankin arewa maso gabas.
Biyo bayan wasu krafe-korafe da wasu sojoji suka yi akan wasu shugabanninsu al'ummar jihar Borno sun bukaci shugaban kasa Jonathan ya kafa kotun bincike na musamman domin ya saurari koke-koken sojojin.
A jihar Borno tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta kara cigaba da ta'adanci hanyar Bama ta zama wata hanya da kodayaushe 'yan bindiga na hallaka masu tafiya cikin motoci.
Biyo bayan tagwayen bamabamai da aka kai akan Jos mutane suna juyayi da tambayar inda makudan kudaden da aka kashe akan tsaro suka shiga
Shugaban kungiyar Kiristoci wato CAN da shugaban Musulmai wato JNI sun yi allawadai da kakkausar murya harin bamabamai da aka kai cikin tsakiyar Jos da ya rutsa da mutane da yawa banda jikata wasu.
Domin Kari