WASHINGTON, DC —
Mata kiristoci daga arewa maso gabas sun fito kwansu da kwarkwatarsu da rera wakar yabon Allah da jaddada tsayawarsu daram cikin addinsu komene ne zai faru, sun yi gangami akan daliban Chibok da aka sace fiye da makonni biyar da suka gabata.
Matan sun taru ne a garin Bauchi domin yin addu'o'i akan lamarin dake faruwa a yankinsu da rokon Allah Yasa a sako daliban nan da aka sace.
Shugabar kungiyar Ruth Kawuwa daga jihar Taraba tayi bayanin dalilin gangamin nasu. Tace sun fito daga jihohin arewa maso gabas ne domin su yi addu'o'i su nuna bakin cikinsu su gayawa Ubangiji Ya ji kukansu a dawo da 'ya'yansu. Sun samu kansu a wani yanayin da basu gane ba sai dai Allah kadai. Ta bukaci a taimakesu da addu'a da inganta tsaro.
Dr. Shaaibu Yanbel shugaban kungiyar kirista ta shiyar arewa maso gabas wato CAN yayi karin haske akan taron. Yace taron juyayi ne domin su kai kokensu ga Ubangiji bisa ga lamuran dake faruwa a yankinsu. Yace " mun gasganta Allah Yana ji. Allah kuma zai amsa" domin kiyayya da gaba dake aukuwa a cikin kasar sun yi allawai dasu. Suna addu'a Ubangiji Ya shiga cikin lamarin Ya kawo ma kasar salama. Suna rokon Allah a samu ingantacen shugabanci a jihohinsu da kasar. Yace yanzu mata ne da yara suke tafiya. Wadannan 'ya'ya fiye da dari biyu da ake garkuwa da su shin wai ana cinsu ne da yaki ko menene. Yace su basu yi tashin hankali da kowace ba a kasar.
Shin wai me suka yi a Najeriya musamman a arewacin kasar inda ko wajen daukan aiki ba'a daukansu. Yanzu ana nemansu sako-sako a yakesu. Addu'ar ke nan da suke so Allah Ya ji. Allah zai ji kuma masu mugunta Allah zai fallasasu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.