Bayan sun bi gwamnan jihar canza sheka zuwa sabuwar jam'iyyar adawa ta APC yanzu an wayi gari 'yan majalisar sun koma PDP kacokan babu kodaya da ya zage a jam'iyyar adawa.
yanzu haka kura ta lafa ana kuma samun kwanciyar hankali a garin Jos.
'Yan Boko Haram sun bakunci garin Alagarno a jihar Borno a Najeriya.
Majalisar Dattawa ta bi sawun majalisar wakilai wadda tuni ta amince da karin wa'adin dokar ta baci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe
Bayan makonni biyar da aka sace dalibai mata kusan su dari uku daga makarantar 'yan mata dake Chibok cikin jihar Borno, daya daga cikin iyayen daliban dake da 'ya'ya biyu ya samu bugun zuciya ya rasu.
Rikici tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya ya zama tamkar ruwandare gama gari kuma yana daya daga cikin lamuran da suka jefa arewa cikin rashin zaman lafiya
Yayin da ake zaton za'a shawo kan 'yan Boko Haram masu haddasa ta'adanci sai gashi wasu bamabamai sun tarwatse a tsakiyar birnin Jos fadar gwamnatin jihar Filato.
Fashewar guda biyu sun auku na a kasuwar dake karban bakoncin dubban jama’a. Jami’an tsaro sunce basu da tabbacin adadin jama’ar da lamarin ya hsafa. An ji karar fashe-fashen daga kilomitoci da yawa, kuma ‘yan kwana-kwana da masu agajin gaggawa sun bazama wajen yayinda mutane suke tserewa.
Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Filato, Chris Olakpe ya tabbatar da cewa a kalla mutane 46 ne suka rasa rayukansu, wasu kuma 45 suka jikkata biyo bayan fashewar Bom a wata kasuwa dake birnin Jos, a Jihar Filato.
Chadi da Kamaru, karnukan farautan kasar Faransa ne don haka dole ne kasar Faransa duk abunda zata yi sai ta saka su a ciki, a cewar wani mai fashin baki.
Misalin karfe uku na rana agogon Najeriya, wasu tagwayen boma-bomai sun fashe a kusa da kasuwar Taminos dake birnin Jos a Jihar Filato, wanda ya jawo asarar rayuka da jikkata wasu.
Domin Kari