Tace sabili da abubuwan dake faruwa basu samu sun sake su yi aikin karatu a makarantarsu ba dalili ke nan da aka kawosu aka hadasu da makarantar 'yan mata ta Maiduguri domin su samu su yi jarabawa ta karshen kammala karatun sakandare. Tace akwai tsaro a Maiduguri fiye da Maonguno musamman makarantar 'yan mata.
Makarantar mata bata da tsaro a Monguno domin haka su ma suna tsoron kada a zo a kwashesu kamar yadda ta faru a Chibok ko kuma a kai masu hari kamar yadda aka yi a Yadin Buni. Tace abubuwan dake faruwa a kauyuka basu da kyan gani. Iyaye da dalibai suna tsoron abun da ka iya faruwa.
Karatu a wurinta yana da mahimmanci domin a zamanin yanzu wanda bashi da ilimi bashi da komi. Tace yanzu ana ganin mata likitoci su ma suna son su zama haka domin su taimaki al'ummarsu da iyayensu. Tace idan ta gama karatu tana son ta zama mai aikin jinya wato nas domin ta taimaki mutanen da basu da lafiya a asibiti.
Wannan daliba ta kira ga gwamnatin jihar Borno da ta tarayya da su yi kokari su kawo karshen tashin tashinar da kungiyar Boko Haram ke haddasawa. Ta kara da cewa abun dake faruwa ya fi shafar mata. Idan ta yiwu a inganta tsaro sosai a kauyukan kananan hukumomi da cikin Maiduguri domin mata su samu sukunin yin makaranta cikin walwala.
Akan sace dalibai 'yanuwanta wannan daliba tace gaskiya abun bai yi dadi ba kuma dare da rana suna addu'a Allah Yasa a sakosu domin lamarin yana firgitar da mutane da yawa. Tace ko su dake cikin Maiduguri har yanzu suna cikin tsoro domin babu wanda ya san abun da zai faru nan gaba. Suna tsoron kad su ma a zo a tafi dasu wata rana domin wadanda aka sace basu san za'a zo a tafi da su ba. Tace yanzu da daliban da iyayen duk suna cikin damuwa.
Ga karin bayani.