Mutanen da suka kauracewa gidajensu, sun ce 'yan Boko Haram, na sintiri tsakanin garuruwa biyu masu nisan kilo mita 50 tsakani, abun da 'yan kungiyar sun kwace ya kai tsawon kilo mita 320 kusa da iyarkar Najeriya da Kamaru.
Ganin yadda 'yan Boko Haram ke ta kwace garuruwa a arewa maso gabashin Nijeriya; 'yan Nijeriya daidaiku da kungiyoyi sun tashi haikan wajen sukar sojojin Nijeriya da kuma hukumomin da alhakin wadata sojin da makamai ya rataya a wuyarsu. To saidai kuma, su ma su na ikirarin cewa ba laifinsu ba ne.
Rikicin 'yan Boko Haram ya sa daruruwan mutane barin gidajen su.
A wata fafatawar da aka yi tsakanin mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya an harbi Kanal Adebayo Obasanjo dan tsoho shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo.
Shugaban kasar Najeriya Ebele Jonathan ya kai ziyara kasar Chadi inda ya gana da shugaban kasar Idris Debi domin hanyoyin da za'a aiwatar da abun da aka shirya a taron Faransa tsakanin shugaban Faransa da shugabannin Najeriya, Chadi,Kamaru da Niger akan fuskantar kalubalen tsaro a yankin.
Wasu da ake zata ‘yan kumgiyar Boko Haram ne sun kai hare kan garin Borote, da ke karamar hukumar Biu dake jihar Borno.
A daren Lahadi ne wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari akan garin Burate dake cikin karamar hukumar Biu a jihar Borno.
Dubban jama'a na cigaba da gudu bayan da 'yan Boko Haram suka sake kwace wasu 'yankuna a jihar Adamawa yayin da suka fatattaki sojojin da aka tura yankin Mdagali da Michika.
Daruruwan mutane ke neman mafaka a wurare da dama
Yayin da mukaddashiyar sakataren harkokin wajen Amurka ke jawabi a Abuja ta sanarda shirin da Aurka keyi domin taimakawa Najeriya da kasashen dake makwaftaka da ita domin yakar Boko Haram.
Tashe-tashen hankula da aka yi a jihar Nasarawa kwana kwanan nan ya haifar da dubban 'yan gudun hijira da suka gudu daga gidajensu sun bazu a sansanoni daban daban inda basa samun taimako daga gwamnati.
Ganin yadda matsalar tsaro ta zama wata babbar annoba a jihar Borno wasu kungiyoyin sa kai da suka hada da civilian JTF da tsofofin sojoji da 'yansanda da na gidan yari da kwastan da 'yanbanga da maharba sun kira taron gangami domin neman daman farauto 'yan kungiyar Boko Haram daga gwamnatin tarayya.
Domin Kari