Shugaban na ziyarar ce a daidai lokacin da ake cigaba da kai farmaki mai zafi a yankin arewa maso gabashin Najeriya inda ake ta batakashi tsakanin sojojin Najriya da 'yan kungiyar Boko Haram.
Idan ba'a manta ba 'yan kwanaki da suka gabata mayakan Boko Haram sun fatattaki sojojin Najeriya har sai da suka arce suka shiga kasar Kamaru.
Domin sanin tasirin da ziyarar shugaban Najeriya zata yi akan matsalar ta'adancin Boko Haram da kasar ke fuskanta, wakilin Muryar Amurka ya tuntubi wani tsohon janaral na soja wato Janaral Abdulrazak Umar. Janaral din yace kwarai ziyarar zata yi tasiri domin ko ba komi abun dake damun kasar ya fito fili karara. Idan da can ana wata rufa-rufa to yanzu abun ya fito. Na biyu idan har za'a saurari shawara to kila su anfana. Idan kuma masu bada shawara suka bayar aka yi watsi da ita wannan ma zai fito.
Wakilin Muryar Amurka ya tambayi Janaral Umar shin ba makamai ya kamata a karawa sojojin Najeriya ba ganin yadda suke korafin basu da isassun kayan aiki domin su samu su yi fito na fito da 'yan Boko Haram wadanda suka kusa cin jihohi biyu ko uku a arewa maso gabashin Najeriya.
Yace soja ba doki ba ne. Ban da kayan aiki akwai kuma maganar kwanciyar hankali. Idan soja zai yi fito na fito da wani kuma yana da tabbas cewa wanda zai hadu dashi shi ma zai yi shakkansa zaiyi kokari. Amma idan sojan nada shakkan cewa ba zai ci nasara ba to komi yawan kayan aiki banza ne. Sai an karfafa masa zuciya, an nuna masa ya san abun da yake yi kuma ya san abun da ya kamata a yi masa kuma an yi masa. Idan ba'a kula dashi ba sai ya shiga tashi harakar.
Shin ko zai kwatanta abun dake faruwa yanzu da rashin kayan aiki da cin hanci da rashawa da kuma ritaya-ritaya da aka yiwa daruruwan janarorin rundunar sojin kasar. Yace abun dake kawo matsala shi ne rashin sanin tabbas kafin a yanke shawara ko hukunci. Kafin a dauki kowane mataki sai an tabbatar da gaskiya an samu dahir an gudanar da bincike kana a dauki kowane mataki. Kuskure ne mutum ya bugi kirji ya fadi abun da bashi da cikakken sani a kai.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.