Wasu da suka tsira da rayukansu sun bayyana cewa da sanyin safiyar Lahadi ne 'yan kungiyar suka sake dira akan yankin Michika da wasu garuruwa akan babura da motoci tare da kafa motocinsu.
Wani da abun ya shafa yace da ya ji harbi sai ya koma maimakon ya shiga Michika ya je wani kauye kusa da Cuwa. Sun shiga garin Cuwa sun kori sojoji sun wuce Michika suna garin Baza.
Mutanen yankin sun shiga wani hali mai wuya. Mutane na fama da yunwa da kishirwa. Wani yace sun shiga garin Baza kuma ba batun sojoji ake yi ba. Yace babu sojoji a kasar yanzu.
Wasu rahotanni na cewa mutane har sun fara gudu daga garin Mubi mahaifar babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janaral Alex Badeh sakamakon nufowa da 'yan Boko Haram din ke kara yi. A garin na Mubi da sojoji da fararen hula duk suna gudu. Tun da 'yan Boko Haram suka isa Baza tana yiwuwa nan da dan lokaci zasu isa Mubi. Sojoji suna ta kansu.
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da halin da ake ciki. Mr Solomon Kumanga sakataren yada labarai na mukaddashin gwamnan jihar yayi karin haske game da matakan da gwamnati ke dauka domin tallafawa wadanda suke gudun hijira
Wani masani a kan harkokin tsaro Dr Abdullahi Wase yace kafin sabbin kayan aiki su iso yakamata a debo sojoji daga wurare daban daban su tafi su kare kasa domin aikin da aka daukesu su yi ke nan. Idan ba'a yi haka ba to za'a cigaba da hallaka mutane.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.