An harbi Kanal Adebayo Obasanjo a kafa to amma baya cikin mummunan yanayi.
Bayanai sun nuna cewa an yi gumurzu tsakanin 'yan Boko Haram da sojojin Najeriya a garin Baza mahaifar babban kwamandan rundunar sojoji dake Jos.
Kawo yanzu garuruwa da dama sun fada hannun 'yan Boko Haram wadanda suka hada da Madagali, Shuwa, Gulak, Michika da kuma sauran wurare dake makwaftaka da Michikan.
Amma akwai rahotanni dake cewa jami'an tsaro na shirin kai farmaki da nufin sake kwato wuraren da suka fada hannun 'yan ta'adan. Wasu da suka tsere daka Gulak da Michika sun bayyana mutane na zaman zullumi domin rashin sanin tabbas domin maharban suna ta harbe-harbe kuma an yi asarar rayuka.
Wani da ya samu ya tsere yace su 'yan Boko Haram suna ta sintiri akan hanya daga Shuwa har zuwa Madagali akan tituna. Kana garin Mubi da a ada ya zama mafakar 'yan gudun hijira yana neman komawa kufai inda dubban jama'a suka tsere yayin da direbobin motocin haya ke tsauwalawa jama'a dake neman fita daga garin. Wasu sun ketara zuwa Kamaru wasu kuma sun arce zuwa Yola.
Wani mazaunin garin yace ko sojoji ma suna takansu ne. Samun mota ma a gudu daga garin yayi wuya domin nera dubu biyar ake biya yanzu daga Mubi zuwa Yola kowane mutum daya ko yaro ne.
Sanadiyar harin yasa hukumar zabe ta dage batun raba katin zabe na din-din-din a wasu kananan hukumomin jihar ta Adamawa. Kwamishanan hukumar zabe yace an daga raba katin ne a arewacin jihar har sai an samu tsaro. Aikin raba kati aiki ne da sai ana da zaman lafiya za'a iya yinsa. Lokacin zabe mutane na iya anfani da katin wucin gadi dake hannunsu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz