'Yan agajin Red Cross sun yi amfani da kayan aikisu wajen kula da wadanda suka raunata a harin bom din makarantar Potiskum.
Rayuka sun salwanta, wasu da dama kuma sun raunata sanadiyar fashewar wani Bom a garin Potiskum,
A wata fira da yayi da Muryar Amurka Sanata Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno yace gwamnatin Shugaba Jonathan ba da gaske ta keyi ba akan yakar kungiyar Boko Haram.
Yanzu haka kimanin ‘yan gudun hijira kimanin dubu biyu ne ke neman mafaka a kano sannadiyyar rikicin Boko Haram a jihohin Borno da Yobe da Adamawa baya ga wadanda rikicin kabilanci a jihar Taraba ya tilasta su kauracewa gidajen su.
Kimanin makonni biyu kennan bayanda wasu mutane suka tayar da Bom a garin Azare dake Jihar Bauci, yau an kara tayar da wani Bom din a garin na Azare har yayi sanadiyar a kalla mutum 14.
Talakawan jihar Adamawa suna kokawa da abun da suka kira halin ko in kula da wasu manyan jihar ke nunawa akan halin da al'ummar jihar suka samu kansu.
Cikin wasu mutane da sojoji suka cafke a Maiduguri da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne an saki waddanda sojojin suka tabbatar ba 'yan kungiyar ba ne
Yayin da arewacin Najeriya ke fama da tashin hankalin da kungiyar Boko Haram ke haddasawa lamarin dake neman durkusar da harkokin kasuwanci a yankin amma hukumar kwastan bata ji a jikinta ba.
Shaidun gani da ido sunce 'yansandan kwantar da tarzoma sun fara kutsawa a wani yunkurin kwato garin Mubi daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka mamaye garin har ma suka canza masa suna zuwa Madinatul Islam.
Yanzu haka dai tuni talakawa a jihar Adamawa sun fara kokawa da abun da suka kira halin ko-in-kulan da suke zargin shugabannin jihar ke nunawa na cigaba da kwashe iyalansu suna ficewa daga jihar.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta tabbatar da cewa a cikin su akwai yara fiye da 6,000
Har wa yau gwamnan na jahar Borno ya godewa matasan sannan yayi tir da halin wadanda ya kira "'yan siyasar Abuja"
Domin Kari